in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da kara sanyawa Rasha takunkumi
2014-07-30 15:31:38 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fitar da wata sanarwa, dake bayyana aniyar kasarsa na kara sanyawa kasar Rasha takunkumi a fannonin makamashi, da aikin soja, da harkokin kudi da dai sauransu.

Sanarwar wadda fadar white house ta fitar a jiya Talata, ta rawaito Shugaba Obama na bayyana sassan da Rashan za ta fuskanci takunkumi a cikinsu, da suka hada da harkokin kudi, da aikin soja, da dakatar da fitar da wasu kayayyakinta na fasahohin musamman a fannin makamashi. A daya bangaren, har wa yau Amurkan ta bayyana dakatar da matakan karfafa aikin fitar da kayayyakinta zuwa Rasha, da kuma na kebe kudade don ci gaban tattalin arzikin Rashan.

Bugu da kari, shugaba Obama ya ce, matakan kakabawa Rasha takunkumin da ake dauka yanzu haka, sun riga sun fara yin tasiri ga tattalin arzkinta, kana sabbin matakan dake biye za su kara yin matsin lamba ga kamfanoni, da wasu mutanen da ke goyon bayan manufofin gwamnatin Rashan game da kasar Ukraine. Har wa yau shugaba Obama ya yi gargadin cewa, idan har Rasha ta ci gaba da bin wannan hanya da take kai yanzu, to ko shakka babu za ta kara yawan asarar da take fuskanta..

Tun bayan barkewar rikicin Ukraine dai dangantakar da ke tsakanin Rasha da Amurka ta kara tabarbarewa. Lamarin da ya sanya Rashan sukar lamirin Amurka bisa zarginta da maida Rashan saniyar ware sakamakon halin da ake ciki a Ukraine.

A wani bangare na daban kuwa, Amurka ta soki Rasha bisa zargin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Ukraine,wanda kuma hakan ya sanya ta hada kai tare da sauran kasashen yammacin duniya wajen sanyawa Rashan takunkumi..

Wannan ne dai matakin da ya janyo matakin da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai EU Jose Manuel Durao Barroso, da shugaban majalisar zartaswar kasashen Turai Herman Van Rompuy suka dauka na fidda wata hadaddiyar sanarwa a jiya Talata, inda suka nuna amincewarsu ga EU da ta kara sanya takunkumi ga Rasha. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China