Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce, babban mai shari'ar kasar Eric Holder zai ziyarci garin Ferguson dake jihar Missouri, game da binciken da za a gudanar don gane da harbe matashin nan bakar fata da wani dan sanda ya yi a 'yan kwanakin baya.
Shugaba Obama wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru da ya gudana a fadarsa ta White House, ya kara da cewa a lokacin ziyarar ta mai shari'a Ferguson, zai zanta da masu bincike na hukumomin tarayya da na jihar. Kaza lika zai gana da masu ruwa da tsaki, a yunkurin da ake yi na dawo da yanayin zaman lafiya da lumana.
Kafin hakan dai sai da Obama ya tattauna da mai shari'ar, da gwamnan jihar Missouri Jay Nixon, da ma wasu 'yan majalissar dattawan jihar.
Mr. Obama ya ce, ya fahimci damuwa da takaicin da kisan matashi Michael Brown ta janyo, wanda hakan ya janyo tarzoma da kaiwa 'yan sanda hari, sai dai a cewarsa, hakan ba zai haifar da komai ba sai tsananta yanayin da ake ciki, tare da yi wa shari'a tarnaki.
Daga nan sai shugaba Obama ya ja hankulan al'ummar garin na Ferguson da su kai zuciya nesa, su kuma rungumi matakan takaita yanayin da ake ciki, maimakon kara tunzura juna. (Tasallah)