A wannan rana, Mr. Froman ya kira wani taron manema labarai, inda ya gabatar da ci gaban taron koli na Amurka da Afirka. Kuma yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da takarar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a nahiyar Afirka, Mr. Froman ya ce, kasar Amurka na maraba da ayyukan zuba jarin da kasashen Sin, India da kuma Turkiya ke yi a Afirka, kuma dukkansu suna nuna himma da kwazo a wannan fanni a halin yanzu.
A sa'i daya kuma, kasar Amurka za ta kuma habaka ayyukan tattalin arziki da cinikayyarta a Afirka. Kuma bisa hanyar kira wannan taron koli na Amurka da Afirka, kasar Amurka za ta ci gaba da tattara kudaden gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu don inganta harkokin zuba jarin kasar a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, ministan harkokin kasuwanci na kasar Amurka Penny Pritzker ya bayyana a wannan rana cewa, kasar Amurka tana fatan ganin ci gaban fitowar kayayyakinta zuwa nahiyar Afirka, domin taimakawa yawan masu matsakaicin karfi a kasashen Afirka. Kuma a halin yanzu, kasar Amurka na kafa sabbin ofisoshin wakilanta a wasu kasashen Afirka da suka hada da Angola, Habasha da dai sauransu, don taimakawa kamfanonin kasar Amurka wajen raya ayyukansu a Afirka. (Maryam)