Shugaba Obama ya tattauna ne da shuwagabannin ta wayar tarho a jiya Asabar 9 ga watan nan ne, kafin daga bisani fadar White House ta fidda wata sanarwa dake cewa shugaba Obama, da David Cameron da kuma shugaba Hollande sun cimma matsaya daya, kan bukatar baiwa fararen hular kasar Iraq da ke tsare a wani babban tsauni taimakon jin kai.
Kaza lika sun shawarta kan yadda za a iya karfafa taimakon da ake baiwa mahukuntan kasar Iraqi, don ta iya samun zarafin fuskantar kalubalen kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta ISIS.
Game da batun kasar Ukraine kuwa, Obama, da Cameron da kuma Merkel sun cimma matsaya guda, ta kin amince da dukkanin matakan da kasar Rasha ke dauka kan Ukraine, bisa hujjar taimakon jin kai, muddin hakan bai samu amincewa daga kasar ta Ukraine ba. Suna masu bayyana matakan na Rasha a matsayin abin da zai iya haddasa babbar illa ga ita kanta kasar ta Rasha.
A daya bangaren kuma, shugaba Obama ya tattauna da firaminista Cameron kan yanayin da ake ciki a yankin Gaza, inda suka yi Allah wadai da hare-haren da aka kaddamar a yankin, bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72.
Shuwagabannin sun kuma yi kira da a dakatar da musayar wuta a yankin ba tare da wani bata lokaci ba.
Bugu da kari, yayin da suka tabo batu kan cutar nan ta Ebola dake barazana ga rayukan jama'ar yammacin kasashen Afirka, shugaba Obama da firaminista Cameron, sun jinjinawa kokarin da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ke yi, wajen dakile yaduwar cutar, tare da alkawarta ba da taimako a wannan fage. (Maryam)