A cikin wata sanarwar da kakakin ma'aikatar shari'a ta Amurrka Brian Fallon ya bayar ya ce, babban attonin janar na kasar ya bayar da umurni ga bangaren shari'ah na kasar a bisa la'akari da bukatun iyalan mamacin da su gudanar da wani zagaye na aune-aune a kan gawar, to amma a wannan karon likitan gwamnatin shi ne zai gudanar da aune-aunen gawar Brown ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakazalika ita ma jihar Missouri tana gudanar da nata aune-aune a kan gawar ta Brown, matashin da aka harbe a yayin da ba ya da mallakin wani makami.
Mutuwar Brown ta haifar da kace-nace a Amurka, a inda wasu ke cewar, dan sandan ya kashe Brown ne, bayan yayi fada da Brown, shi kuma dan sandan yayi zargin cewar ya kama Brown ne yana sata a wani kanti, akwai kuma masu cewar an kashe Brown ne a yayin da ya daga hannuwansa sama, watau alamun saranda, kuma ya roki dan sandan da kar ya harbe shi.
Mutuwar ta Brown ta haifar da kwanaki da yawa na munanan tashe-tashen hankula a Ferguson.(Suwaiba)