in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta taimakama kasashen Afrika a ayyukan wanzar da zaman lafiya.
2014-08-15 11:00:10 cri
Gwamnatin Amurka za ta bada kudi don taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya a Ghana da wassu kasashen Afrika guda biyar, in ji Ministan harkokin wajen kasar Ghana Hannah Serwa Tetteh.

A lokacin wani ganawa da manema labarai a Accra, babban birnin kasar, Madam Hannah Serwa Tetteh ta yi bayanin cewa, Amurkan da hadin gwiwwar gwamnatocin Afrika sun tsaida shawarar samar da taimako ga kasashe 6 a nahiyar da kudi dala miliyan 110 a kowane shekarar har tsawon shekaru 3 zuwa 5 bisa shirin wanzar da zaman lafiya na gaggawa.

Sauran kasashen biyar da zasu amfana da wannan hadin gwiwwa sun hada da Senegal, Ethiopia, Tanzaniya da kuma Uganda.

Manufar wannan taimako in ji ministan harkokin wajen ta kasar Ghana, ita ce domin taimakawa a samun kai dauki na gaggawa ga duk wani tashin hankali da ka iya tasowa kwatsam a nahiyar.

Amurka dai ta kara shiga cikin ayyukan taimakawa sojojin kasashen nahiyar Afrika wajen yunkurin kawar da masu tsattsauran ra'ayin addini kwanan nan, ta hanyar horas da sojoji da 'yan sanda sama da 250,000.

A lokacin babban taron kasashen Afrika da Amurka makon da ya gabata a Birnin Washington, shugaba Barrack Obama na Amurkan ya sanar da sabon shirin na zuba kudi dalar Amurka miliyan 110 a cikin shekaru 3-5 domin taimakawa kasashen Afrika 6 wajen maida martani cikin gaggawa a duk wani hali na tashin hankali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China