Da take hira da mujallar Atlantic mai fitowa wata wata, Uwargida Clinton ta yi amfani da kalamai masu kaushi na bayyana irin koma bayan da aka samu sakamakon tsari maras ma'ana na Obama da ya yi shawarar shiga cikin rikicin tun da farko a Syria wanda a ciki 'yan adawa suke kokarin hambarar da Shugaba Bashir Al-Assad.
Ta ce, raunin da aka samu tun da farko na kasa gina rundunar da za ta iya fada sosai ta kare jama'ar ta wadanda tun farko su ne suka tada wannan tashin hankali na adawa da Assad, akwai sojojin masu son bin addinin Islama, akwai masu ra'ayin ba ruwansu da addini, akwai komai ma a yankin gabas ta tsakiya, rashin gina wadannan kungiyoyin ya bada gibi mai yawa wanda sojojin masu kaifin addini suka cike shi yanzu haka.
Mayakan Sojojin Amurka da jiragen sama marasa matuka suna ta kai hare hare a kan jihohin da kungiyar mai kaifin addinin Islama ta kame ta mayar jihohin musulunci, da kuma Levant dake arewacin Iraq na tsawon kwanaki uku a jere yanzu haka tun lokacin da Obama ya bada umurnin kai hari a ranar Alhamis da ta gabata domin bada kariya ga Amurkawa da kuma aiwatar da ayyukan jin kai.(Fatimah Jibril)