Kafofin watsa labaru na kasar Faransa sun tsamo labari cewa, bankin Paris da mahukuntan kasar Amurka sun cimma daidaito kan yarjejeniyar samun sulhuntawa a tsakaninsu. Bisa yarjejeniyar, bankin Paris ya amince da laifinsa tare da biyan tarar da yawansu ya kai dala biliyan 8.9 don hana hukumar dokokin shari'a ta kasar Amurka ta gurfanar da shi a gaban kotu. Wannan ne zai kasance tara mafi yawa da kasar Amurka ta ci bankunan sauran kasashe.
An zargi bankin Paris da aikata laifin saba wa umurnin hana yin cinikin dala da Iran, Sudan, Cuba da sauran kasashe da Amurka ta sanya ma takunkumi tun daga shekarar 2002 zuwa 2009. Ko da yake bai saba wa dokokin duniya ba, amma tilas ne a yi cinikin dala ta gidan hada-hadar kudi na Amurka, sabo da haka ya kamata ya bi dokokin kasar Amurka. (Zainab)