Obama wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba ya kuma bayyana kisan da 'yan ISIS din suka yiwa James Foley, a matsayin wani lamari da ya yi matukar bakanta ran jama'a.
A daya hannun kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Marie Harf ta ce, bisa kididdigar da kasar ta yi, an ce, yanzu haka akwai dakarun sa kai masu tsattsauran ra'ayi na kasashen duniya daban daban sama da dubu 12 cika hadda Amurkawa, dake kasashen Iraqi, da Syria da sauransu. Dakarun da a cewar Harf, na iya haddasa barazana matuka ga Amurka bayan sun koma gida.
A sa'i daya kuma, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi suka mai tsanani game da sare kan dan jaridar nan James Foley, da 'yan kungiyar ISIS suka yi, ya kuma jaddada cewa wajibi ne a gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi gaban kuliya. (Maryam)