Ko da yake kwamitin ya amince da kokarin da Amurka ta yi wajen kawar da wannan tunani, amma wasu mambobin sun nuna cewa, tun bayan da aka tantance yadda Amurka ta yi a wannan fanni a shekarar 2008, har zuwa yanzu an kasa samun ci gaba wajen kafa doka don kawar da ra'ayin nuna bambancin launin fata. Ban da wannan kuma, ana samun irin wannan ra'ayi a fannonin samar da guraben aikin yi, yin sayayyen gidaje, shiga makarantu masu zaman kansu da dai sauransu.
Kazalika, wasu mambobin sun bayyana cewa, rabin masu aikata laifi da aka yanke musu hukuncin kisan 'yan asalin Afrika ne a shekarar 2001. A 'yan shekarun nan kuma, Amurkawa 'yan asalin Afirka 140 wadanda aka yanke musu hukuncin kisan, daga baya kuma an gano cewa, lallai ba su aikata laifi ba. Duk wadannan abubuwan sun nuna a zahiri cewa, akwai bambancin launin fata a cikin tsarin shari'ar Amurka.
Bugu da kari, wadannan mutane su kan fuskanci harin bindiga da a kan kai musu a Amurka, kuma a kan ci zarafin 'yan mata na wadannan jinsi, sannan a kan tilastawa kananan yara 'yan asalin Latin Amurka da na Afrika da ba su baligai ba su yi aikin karfi. (Amina)