Sakataren harkokin wajen kasar Burtaniya William Hague ya kai ziyara a kasar Iraki a ranar 26 ga wata, inda ya yi shawarwari tare da shugabannin kasar kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma yanayin siyasa da tsaro da kasar ta Iraki ke ciki. A gun taron manema labaru bayan shawarwarin, Hague ya kalubalanci shugabannin kasar Iraki da su hada kai da sa kaimi tare da kafa sabuwar gwamnati don tinkarar barazanar da ake fuskanta. Ya kuma ce, a halin yanzu, abu mafi muhimmanci su ne rukunonin siyasa daban daban su jingine duk wani bambancin ra'ayi, kana da hada kai wajen kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi kowa da kowa a kasar. A nasa bangare, firaministan kasar Iraki Nourial Maliki ya bayyana cewa, muddin ana bukatar a warware rikicin kasar Iraki, ya kamata a cimma nasarar yaki da dakaru masu ta'adda, da gudanar da taron sabuwar majalisar dokokin jama'ar kasar bisa lokacin da aka tsara don ingiza shirin mika mulki a kasar.
A wannan rana kuma, ministan harkokin wajen kasar Rasha Lavrov ya bayyana yayin da yake zantawa ta wayar tarho tare da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Kerry cewa, Rasha da Amurka za su kiyaye yin shawarwari kan batun Iraki. Kana Kerry ya yi bayani game da ziyararsa a kasar Iraki, inda ya ce, karuwar ayyukan ta'addanci a kasar Iraki sun tsanantar da halin tsaro a kasar. Kuma kasashen biyu suna sa lura sosai kan tsaron yankunan dake fuskantar barazanar masu tsattsauran ra'ayi a kasar Iraki. (Zainab)