An shafe awa daya ana gudanar da shawarwari, daga bisani wakilin dindindin na kasar Birtaniya dake MDD wadda ke rike da shugabancin kwamitin a wannan wata, Mr Mark Lyall Grant ya kira taron manema labaru bayan tattaunawar, inda ya bayyana takaici kan rashin samun matsaya daya.
Wakilin dindindin na kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya ba da jawabi bayan tattaunawar domin bayyana matsayin da Rasha ta dauka na cewa, Rasha na kokarin baiwa Ukraine tallafin jin kai da take bukata, kuma zargin da Ukraine take zance ne maras tushe.
Mista Churkin ya jaddada cewa, ayarin motocin kasar suna dauke da kayayyakin tallafi, kuma da kakkausar murya ya yi Allah wadai da wasu kasashen yamma wadanda suka dauki ra'ayin ba ruwansu kan mawuyacin halin da Ukraine ke fuskanta, har ma suna neman kawo katsalandan kan taimakon da Rasha ke bayar.
Kafofin yada labaru sun ba da labari cewa, ayarin motocin Rasha sun isa gabashin Ukraine a ran 22 ga wata dauke da abinci kimanin ton 2000 da ruwan sha da abincin jarirai da magunguna. (Amina)