in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Ukraine sun ce, suna son tsagaita bude wuta
2014-08-10 16:57:43 cri

Ranar 9 ga wata, firaminista Vitaliy Zaharchenko na jamhuriyar Donetsk ta Ukraine ya ce, bisa zummar hana tsanancewar yanayin jin kai da ake fuskanta a yankin Donetsk, dakarun jamhuriya sun yi shirin tsagaita bude wuta.

Zaharchenko yana kuma fatan kungiyoyin kasa da kasa za su matsa wa gwamnatin Ukraine lamba domin warware matsalar jin kai a yankin. Sai dai ya jaddada cewa, idan mahukuntan Ukraine suka ci gaba da daukar matakin soja, to komai wuya, dakarun za su ci gaba da gwagwarmaya.

Jim kadan bayan wannan sanarwa ne kuma aka harba wasu makamai a birnin na Donetsk. Harin da dakarun Donetsk da na rundunar sojan Ukraine din suka zargi juna da laifin kaddamarwa.

A dai wannan rana, shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya bayyana cewa, gwamnatinsa tana tunanin aikewa da kungiyar ba da agaji zuwa jihar Luhansk. Bisa labarin da aka bayar a kan shafin intanet na shugaban Ukraine, an ce, da daren wannan rana, Poroshenko ya buga wayar tarho ga shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden, inda ya sanar musu shirin gwamnatinsa na ba da agaji a kudu maso gabashin Ukraine, ya kuma gayyaci Jamus da Amurka da su shiga tawagar ba da agajin. A nasu bangaren madam Merkel da mista Biden sun ce, tilas ne hukumar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta kafa irin wannan tawagar ba da agaji, wadda kuma za ta samu amincewa daga gwamnatin Ukraine. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China