Haka kuma, rahotanni na cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai je Crimea cikin 'yan kwanaki masu zuwa, bugu da kari, firaministan kasar Dmitri Medvedev da galibin 'yan majalisar dokokin kasar Rasha ta Duma za su raka Mr. Putin zuwa Crimea. Dangane da lamarin, wasu na ganin cewa, kasar Rasha tana son nuna matsayinta ne kan dukkanin matakan da ta dauka, ko da dangantakar dake tsakaninta da kasar Ukraine, kuma tsakaninta da kasashen yammacin duniya ta kara tsananta, duk kuwa da takunkumin tattalin arzikin da Amurka da wasu kasashen yammaci ke ci gaban da kakaba mata. (Maryam)