Da yake zantawa da wata kafar radiyon kasar ta Rasha a birnin Moscow, mai magana da yawun fadar gwamnatin Rashan Dmitry Peskov, ya ce zargin da ake yiwa Rasha ba shi da tushe balle makama.
Wannan zargi dai na baiwa mayakan na gabashin Ukraine tallafin makamai, ya biyo bayan kalaman firaministan jamhuriyar Donetsk Aleksandr Zakharchenko, wanda yayin wani taro ya bayyana cewa mayakansa, sun karbi agajin wasu motocin yaki 150, koda yake bai bayyana daga ina suka samu tallafin ba.
Da ma dai kasashen yamma sun sha zargin Rasha da taimakawa 'yan tada kayar baya a wannan yanki na gabashin Ukraine, laifin da Rashan ta sha musantawa.
A baya bayan nan ma wani rukuni na kayayyakin jin kai da Rashan ta shirya shigarwa Ukraine ya janyo kace-nace, inda wasu ke zargin mai yiwuwa ne Rashan, ta fake da hakan ta shigar da makamai cikin Ukraine.
Game da hakan Rasha ta gayyaci wakilan hukumar tsaro da hadin kan Turai zuwa kan iyakarta cikin watan Yuli, domin tantance kayayyakin da ake tababa a kan su. (Saminu Alhassan)