in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Rasha za ta hada gwiwa da kungiyar Red Cross wajen tura ayarin motocin jin kai zuwa kasar Ukraine
2014-08-12 16:06:51 cri
Shugaban kasar Rasha Vładimir Putin ya bayyana a ranar litinin 11 ga wata, cewar kasarsa za ta hada gwiwa da kungiyar Red Cross wajen tura ayarin motoci na jin kai zuwa kasar Ukraine.

Bisa labarin da aka bayar a shafin internet ta shugaba Putin, an ce shugaban ya bayyana hakan lokacin da ya buga wayar tarho ga shugaban kwamitin kungiyar EU José Manuel Durão Barroso.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov wanda ya yi ma manema labarai Karin haske a kan batun ya ce, za a gudanar da aikin tura ayarin motocin jin kai cikin hanzari a karkashin jagorancin kungiyar Red Cross.

Mr Lavrov daga nan sai jaddada cewa, wannan aiki na kasar Rasha ne kuma ra'ayin da kasar Amurka, Ingila da Jamus suka bayyana wai babu butakar samar da taimakon jin kai ga gabashin kasar Ukraine ba shi da tushe. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China