A ranar 7 ga wata, sojojin Ukraine sun sanar da cewa, sun riga suna rike da iyakar da ke tsakaninta da Rasha.
Bisa labarin da muka samu, an ce, tun bayan da sojojin gwamnati suka maido da daukar matakan soja a gabashin kasar a watan Yuli, ya zuwa yanzu sun kwace birane da garurruwa da dama daga hannun dakarun a wannan yanki. Bisa ga ci gaban da aka samu, mataki na gaba a sojojin gwamnati za su dauka shi ne, yin kangiya a birnin Donetsk, babban birnin jihar Donetsk, da kuma birnin Luhansk, babban birnin jihar Luhansk, don tilastawa dakarun jama'a sun ajiye makamansu.
Ofishin kakakin babban sakataren MDD ya bayyana a ranar 7 ga wata cewa, game da halin da ake ciki a gabashin Ukraine, Ban Ki-Moon ya yi zargi kan ayyukan keta dokoki da dakarun suka aikata, a sa'i daya kuma ya yi kira ga mahukuntan Ukraine da su yi hakuri, da tabbatar da ba da kariya ga fararren hula da ke wadannan wurare.
Ban Ki-Moon ya ci gaba da cewa, daukar matakan soja kawai, ba zai taimaka wajen warware matsala ba, abu mai muhimmanci shi ne bangarori daban daban da abin ya shafa su tsagaita bude wuta da daina nuna karfin tuwo da daidaita rikicin cikin lumana ta hanyoyin siyasa da diplomasiyya. (Danladi)