in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ukraine ya amince da yin shawarwari kan sassauta halin da ake ciki a gabashin kasar
2014-07-04 14:46:16 cri
An ci gaba da samun tashe-tashen hankali a gabashin kasar Ukraine a ranar alhamis 3 ga wata, inda shugaban kasar Petro Poroshenko ya bayyana cewa, ya amince da yin shawarwari kan sassauta halin da ake ciki a gabashin kasar.

An bayyana a shafin internet na shugaban kasar Ukraine a wannan ranar ta alhamis cewa, lokacin da shugaba Poroshenko ya buga wayar tarho ga mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya bayyana cewa, idan bangarori da abin ya shafa sun tabbatar da tsagaita bude wuta, da sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan kuma kungiyar kiyaye tsaro da hadin gwiwa ta kasashen Turai ta OSCE ta sa ido kan iyakar kasa a tsakanin Ukraine da Rasha, gwamnatin sa za ta tsagaita bude wuta da yin shawarwari kan sassauta halin da ake ciki a gabashin kasar ba tare da sharadi ba.

Bugu da kari, shugaban kasar Faransa François Hollande, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun yi shawarwari ta wayar tarho kan halin da ake ciki a kasar Ukraine a ranar alhamis. Sakamakon haka hukumar watsa labaru ta shugaban kasar Rasha ta bayar da wata sanarwa, inda ta ce, shugaba Putin ya bayyana aniyarsa ta ganin an dakatar da bude wuta a yankin gabashin kasar Ukraine, bisa hadaddiyar sanarwar da aka bayar bayan shawarwari a tsakanin ministocin harkokin waje na wadannan kasashe hudu. Kuma ya ce kungiyar tuntubar juna kan batun Ukraine da ta hada da Ukraine, Rasha da kungiyar OSCE za ta tattauna batun kafin ranar asabar din nan 5 ga wata.

Haka zakila, Madam Angela Merkel na Jamus da shugaban kasar Amurka Barack Obama sun tattauna kan halin da kasar Ukraine ke ciki ta wayar tarho a wannan ranar ta alhamis, inda suka yi kira ga dakaru masu zaman kansu dake gabashin kasar Ukraine da gwamnatin kasar su dakatar da bude wuta nan take, sannan suka bukaci kasar Rasha da ta sa kaimi ga bangarorin dake yaki da juna na kasar Ukraine na ganin sun tattauna tsakanin su. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China