in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar NATO ta sanar da goyon bayan Ukraine a fannin siyasa
2014-08-08 10:58:33 cri
Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ziyarci kasar Ukraine a jiya Alhamis 7 ga wata, inda ya bayyana aniyar kungiyar NATO ta goyon bayan kasar ta Ukraine a fannin siyasa.

Bisa labarin da gwamnatin kasar Ukraine ta fitar a shafinta na internet, an ce, firaministan kasar Ukraine Seniy Yatseniuk ya gana da Mr. Rasmussen a wannan rana, inda suka yi alkawarin cewa, kungiyar NATO za ta ba da taimakon kayayyaki da fasahohi ga kasar Ukraine wajen inganta aikin tsaron kasar.

Haka kuma, Mr. Yatseniuk ya nuna godiyarsa matuka ga matsayin da kungiyar NATO ta dauka kan batun Ukraine. A nasa tsokaci kuma, Mr. Rasmussen ya ce, kungiyar za ta tsara wasu matakai don fuskantar yanayin ci gaban kasar Ukraine.

Haka zalika, bisa labarin da shugaban kasa ta Ukraine ya fitar a shafinsa na Internet, ya nuna cewa, shugaban kasar Petro Poroshenko ya baiwa Mr. Rasmussen lambar yabo a wannan rana, don nuna yabo kan manyan gudummawa da Mr. Rasmussen din ya samar wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kungiyar NATO da kasar Ukraine cikin shekaru da dama da suka gabata. Shugaban Poroshenko ya bayyana cewa, dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Ukraine da kungiyar NATO za ta ba da tabbaci a kokarin da ake na gudanar da kwaskwarima a kasar da kuma kiyaye cikakken yankin kasa. Sa'an nan kuma, Mr. Rasmussen ya ce, kungiyar ta goyi bayan kokarin kasar Ukraine na kafa wata kasa mai bin tsarin dimokuradiyya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China