in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ukraine za ta ba da jagora wajen binciken hadarin jirgin saman Malaysia MH17
2014-07-19 16:37:21 cri

Liow Tiong Lai, ministan harkokin sufuri na kasar Malaysia ya bayyana a ranar 18 ga wata cewa, bisa tanade-tanaden da ke cikin manufofin hukumar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa, an ce, gwamnatin kasar Ukraine ce za ta ba da jagora wajen yin binciken hadarin jirgin saman kasar Malaysia MH17, ya kuma yi kira ga sassa daban daban da su hada kansu, a kokarin tabbatar da kammala aikin yadda ya kamata, tare da kiyaye cikakken wurin da jirgin ya fadi.

Sa'an nan kuma dakarun da ke gabashin kasar Ukraine sun yarda da yin hadin gwiwa da gwamnatin kasar wajen binciken hadarin, sun kuma yi alkawarin tabbatar da tsaron masu bincike wadanda za su shiga wurin da jirgin ya fadi domin yin binciken.

Har wa yau bisa labarin da ma'aikatar kula da ayyukan more rayuwar jama'a ta Ukraine ta bayar, an ce, a ranar 18 ga wata, Ukraine ta gayyaci kasashen Malaysia, Holland, kamfanin Boeing, hukumar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Turai, kwamitin kungiyar tarayyar Turai da kwamitin kula da tsaron sufuri na kasar Amurka, da su ba ta taimako wajen binciken dalilin aukuwar hadarin jirgin.

Hukumar binciken hadarin jiragen saman fasinja ta Ukraine ta riga ta kafa wani kwamitin musamman domin yin binciken hadarin, kuma mambobin kwamitin sun riga sun tashi zuwa wurin aukuwar hadarin.

Haka zalika, kasashen Jamus, Belgium Indonesia, Girka da kuma kungiyar tarayyar Turai da wasu kasashe sun yi kira da a gano dalilin aukuwar hadarin cikin hanzari. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China