Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya zanta da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ta wayar tarho a jiya Laraba. Yayin tattaunawar tasu Mr. Ban ya jaddada wajibcin kara yin kokari a fannin siyasa da diplomasiyya, domin warware rikicin Ukraine cikin lumana.
A dai wannan rana ofishin kakakin babban magatakardar MDD ya fidda wata sanarwa, wadda ke dauke da fatan Mr. Ban game da daukar matakan tabbatar da shirin wanzar da zaman lafiya, wanda shugaba Petro Poroshenko ya gabatar.
Kaza lika, sanarwar ta bayyana ra'ayin MDD don gane da halin jin kai da kasar ke ciki, tare da fatan samun hadin gwiwa daga kasashen duniya domin bayar da taimakon da ya dace.
A daya bangaren kuma kasar Rasha ta gabatar da shawarar baiwa gabashin Ukraine tallafin jin kai a makon da ya gabata, bisa jagorancin kwamitin kungiyar agaji ta Red Cross, ko da yake wasu kasashen yamma ciki hadda Amurka, da Birtaniya da Jamus da sauransu, sun nuna shakku kan wannan shawara.
Game da wannan batu mataimakin direktan a ofishin shugaban kasar Ukraine Valeriy Chalyy, ya bayyana cewa, kasar Ukraine ba za ta yarda da shigar ayarin motocin ba da tallafin jin kai na kasar Rasha ba, sai dai za a iya jibge wadannan kayayyaki cikin motocin kungiyar Red Cross, a wani wurin dake kan iyakarta da Rasha.
Ukraine dai ta nuna cewa, za ta dauki duk wani matakin jin kai a matsayin harin soja muddin dai ba a shawarce ta game da hakan ba. (Amina)