A wani ci gaban kuma, ministan ma'aikatan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya jaddada a birnin Moscow cewa, babu wasu sharudda da suka gindaya cikin yarjejeniyar da ministocin harkokin wajen kasashen Jamus, da Faransa, da Rasha da Ukraine suka cimma ran 2 ga watan Yuli.
Bugu da kari, wani rahoto daga fadar shugaban kasar Faransa na cewa, shugaban kasar Francois Hollande da takwararsa ta kasar Jamus Angela Merkel sun yi zantawa ta wayar tarho, inda suka jaddada muhimmancin tsagaita bude wuta a gabashin kasar Ukraine. Shugabannin sun kuma amince da hadin kai da kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta kasashen Turai domin kiyaye yankunan dake kan iyakar kasashen Rasha da Ukraine, da cimma burin sakin daukacin mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Maryam)