Sakataren hukumar tsaron kasar Ukraine Andrey Parubii ya bayyana a wannan rana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kwace ikon yankuna 23 cikin yankuna 36 na jihohin biyu, yanzu yawan yankunan da ke hannun 'yan aware ya ragu sosai a cikin mako guda da ya wuce.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Alexander Lukashevich ya bayyana wa taron manema labaru a wannan rana cewa, aikin dake gaban kome wajen warware rikicin Ukraine shi ne aiwatar da yarjejeniyar da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Jamus, Faransa da Ukraine suka cimma a ranar 2 ga wata, da kuma tsagaita bude wuta cikin hanzari.
A nata bangare ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ta yi allah wadai da harin da sojojin kasar Ukraine suka sake kai kan tashar binciken ababan hawa dake kan iyakar Rasha da Ukraine. (Zainab)