in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu masu bincike kan jirgin saman nan na Malaysia sun janye bisa dalilai na tsaro
2014-08-03 17:23:30 cri
Wasu rahotanni na cewa har ya zuwa ranar Asabar 2 ga watan nan, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin da jirgin saman fasinjan nan na kasar Malaysia mai lamba MH17 ya fadi.

Rahotannin baya bayan nan dai na cewa, wasu daga kwararrun dake gudanar da aikin bincike kan hadarin sun janye daga wurin, bisa dalilai na tsaro, bayan da gungun masanan na kasa da kasa da masu sa ido daga kungiyar tsaro ta Turai suka fara aiki a yankin.

An dai labarta cewa, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta zanta ta wayar tarho sau da dama da shugaba Putin na Rasha, da nufin shiga tsakani kan rikicin dake aukuwa tsakanin Rasha da Ukraine, da ma batun tsara shirin tabbatar da zaman lafiya a gabashin Ukraine.

Ajiya ne dai rukunin ma'aikata dake kunshe da masu bincike 70, da masu sa ido na kungiyar tsaron Turai 8 suka isa wannan wuri domin fara aiki, sai dai bada dadewa ba aka rika jin amon bindigogi, sakamakon wani fada da ya kaure tsakanin sojojin Ukraine da dakaru 'yan a ware dake gabashin kasar, a wani wuri dake da tazarar kilomita 2, da inda ma'aikatan ke gudanar da bincike. Lamarin da ya tilasta wasu daga cikin su janyewa daga wurin.

Kafofin yada labarun kasar Jamus da na Birtaniya dai sun gabatar da bayanai, dake cewa shugabar gwamnatin Jamus, da shugaba Putin na Rasha, suna gudanar da shawarwari game da shirin tabbatar da zaman lafiya a Ukraine. Shirin da ya kunshi burin da ake da shi na Rasha ta amince, ta dakatar da goyon bayan dakaru 'yan a ware dake gabashin Ukraine, ta kuma taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya a kan iyakar.

Har wa yau shirin na fatan Rasha za ta ci gaba da bada iskar gas ga Ukraine.

A bangaren kasashen duniya kuma, ana fatanYayin da kasashen duniya za su amince da shigar Crimea cikin Rasha, kana Ukraine ta kauracewa shiga kungiyar NATO.

An dai labarta cewa, Merkel ta yi shawarwari na tsahon rabin sa'a da shugaba Putin domin cimma wannan buri.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China