A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro a fili dangane da batun Gabas ta Tsakiya, inda Liu Jieyi ya bayyana cewa, kasar Sin na goyon bayan shawarwarin zaman lafiya da ake yi a halin yanzu tsakanin Falesdinu da Isra'ila, kuma abu mafi muhimmanci ga shawarwarin dake tsakaninsu shi ne, bangarorin biyu su amince da ikon juna, tare da nuna fahimtar juna.
Ya ce, a halin yanzu dai, ya kamata a dakatar da gina matsugunan Yahudawa, kawo karshen tashe-tashen hankali da kuma kawar da duk wani hani da aka yi wa yankin Gaza daga dukkan fannoni, ta yadda za a iyar samun ci gaban shawarwarin.
Haka zalika, mista Jieyi ya kara da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta dukufa wajen ciyar da shawarwarin zaman lafiyar tsakanin bangarorin biyu gaba, don kiyaye yanayin tsaro da na karko a yankin Gabas ta Tsakiya. Kasar Sin na fatan bangarorin hudu da batun Gabas ta Tsakiya ya shafa, wato MDD, kasar Amurka, kungiyar tarayyar kasashen Turai da kuma kasar Rasha za su dauki matakai yadda ya kamata don ciyar da shawarwarin gaba. Kasar Sin ta kuma nuna goyon baya ga kwamitin sulhu na MDD da ya ci gaba da ba da taimako kan wannan batun.
Bugu da kari, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen ciyar da shawarwarin zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila gaba bisa ra'ayoyi guda hudu da shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar, don ba da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya daga duk fannoni a yankin Gabas ta Tsakiya. (Maryam)