Taron na ranar Asabar ya biyo bayan amincewar da Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falesdinu suka yi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'oi 12.
Taron ministocin ya kuma kira wata ganawa da 'yan jaridu a wannan rana, inda a madadin sauran ministocin, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya bayyana cewa, an cimma matsayi guda kan kokarin da ake yi na dakatar da bude wuta a yankin Gaza.
Fabius ya kara da cewa mahalarta taron sun kuma yi kira da a tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta a yankin, domin kaiwa ga cimma dauwamammen zaman lafiya, wanda zai dace da moriyar bangarorin biyu.
Har wa yau bisa labarin da aka samu, an ce, da yammacin ranar ta Asabar, dubun-dubatar mutane sun yi dandazo a babban dandalin dake birnin Faris, domin nuna rashin amincewa da matakan sojin da Isra'ila ke dauka a yankunan al'ummar Falasdinawa. (Maryam)