Mr. Wang ya kuma bayyana cewa, ra'ayin kasar Sin kan batun Isra'ila da Falesdinu shi ne, bangarorin biyu su shata iyakokinsu bisa iyakar da aka tsara a shekarar 1967, ta yadda gabashin birnin kudus zai kasance babban birnin kasar, Falesdinu ta kasance kasa mai 'yancin kai, sa'an nan kuma a sami zaman lafiya tsakanin kasar Isra'ila da kasar Falesdinu, haka kuma, za a tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Kasar Sin za ta ci gaba da dukufa don cimma wannan buri. (Maryam)