Mahukuntan kasar Sin sun alkawarta tattaunawa da hukumomin daban daban, tare da daukar matakan da za su dace wajen raya sha'anin cinikayyar shige da fice cikin karkoyadda ya kamata.
Mataimakin ministan cinikin gidan kasar Sin Zhan Zhong Shan ne ya bayyana hakan, yayin bikin baje kolincinikin birnin Guangzhou (Canton Fair) karo na 115 da aka bude a yau Talata. Mr Zhong ya kuma kara da cewa, Sin ta kai matsayin farko a duniya, a fagen cinikayyar kayayyaki a shekarar 2013, sakamakon tsarin bude kofa ga kasashen waje da take aiwatarwa. Har ila yau Zhong ya bayyana aniyar gwamnatin kasar Sin, ta hada kai da ragowar hukumomi domin sa kaimi ga kyautata manufofin cinikayya, da hada-hadar kudade, da haraji da kuma samar da damar bunkasuwar cinikayya, ta yadda za a samar da wani yanayi mai kyau ga bunkasuwar kamfanonin dake wannan sashe.
Dadin dadawa, a cewar sa bisa hadin kan da ake yi da sauran hukumomi, za a gaggauta nazari da fidda wasu shawarwari, game da kara karfin yin takara a fannin cinikayyar shige da fice, ta yadda a nan gaba za a kai ga cimma burin raya wannan sha'ani yadda ya kamata. (Amina)