in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Laberiya ta jinjinawa kasar Sin game da taimakon kayan yaki da Ebola
2014-08-17 17:43:01 cri

Mahukuntan kasar Laberiya sun bayyana matukar godiya game da taimakon kayayyakin yaki da cutar Ebola da kasar Sin ta samarwa kasar.

Rahotannin baya bayan nan dai sun nuna cewa kayayyakin tallafin da kasar ta Sin ta aike zuwa Laberiyan sun isa kasar a daren ranar Litinin din data gabata.

Kafafen yada labarun Laberiyan sun rawaito mahukuntan kasar na bayyana yadda wadannan kayan tallafi na Sin suka karfafi kokarin da ake yi na yaki da cutar ta Ebola.

Game da hakan wadannan kafafen yada labaru sun rawaito shugabar kasar Laberiyan Ellen Johnson na cewa, ko da yake lardin Yunnan na kasar Sin ya sha fama da girgizar kasa, hakan bai hana kasar Sin tallafawa kasar ta da kayayyakin jiyya a lokuta da dama ba. Hakan a cewar Johnson ya nuna irin aminci dake tsakanin Sin Laberiya, da ma irin kwazon kasar ta Sin wajen sauke nauyin dake kan ta game da al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Kaza lika jaridar " The first Page" ta Afirka ta fidda labari game da isar wadannan kayayyakin, inda ta rawaito wani jami'in rukuni na musamman mai kula da cutar Ebola a kasar na cewa, taimakon da Sin take bayarwa ya shaida zumuncin dake tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da ma jama'arsu, a hannu guda kuma Sin ta gwada kyakkyawan misali a wannan fanni.

Bugu da kari wata jaridar ta daban ta fidda wani sharhi da ta yiwa take da "Taimakon da Sin take bayarwa ya shaida sahihiyar abokantaka tsakanin kasashen biyu", sharhin da ya nuna cewa, Sin ta samar da kayayyakin tallafi, tare da tura masanan masu aikin jiyya uku zuwa kasar, matakin da ya bayyana kasar ta Sin, a matsayin kasa mai karfi dake sauke nauyin dake wuyanta yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China