in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta kebe dalar Amurka miliyan guda domin yaki da cutar Ebola
2014-08-15 10:37:53 cri
Kwamitin tarayyar Afrika ya bayyana niyyar tallafawa kokarin da kasashen duniya suke a yanzu haka na yaki da annobar cutar Ebola a yammacin nahiyar Afrika, tare da kebe dalar Amurka miliyan guda daga asusunta na jin kai.

A cewar wata sanarwa ta kungiyar AU da aka fitar a ranar Alhamis, kwamitin tarayyar Afrika da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (OMS) sun gayyaci kasashe mambobin kungiyar AU da su kara bada taimakon kudi ga asusun jin kai na AU da kuma asusun gaggawa na kiwon lafiyar jama'a a nahiyar Afrika bisa burin taimakawa kasashen da wannan cuta ta fi shafa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China