Kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta WHO ta sanya kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afirka cikin jerin kasashen da mai iyuwa za su yi fama da yaduwar cutar Ebola, lamarin da ya cusa damuwa matuka ga sauran kasashen da cutar ba ta shiga ba a halin yanzu, sabo da mai iyuwa ne, cutar Ebola za ta yadu daga yammacin kasashen nahiyar Afirka zuwa sauran kasashen. Kana, a halin yanzu, ba a samu bullar cutar a kudancin kasashen Afirka ba, amma dangane yadda jama'a ke kai koma tsakanin kasashen, ya sa kasashen da abin ya shafa suke ci gaba da karfafa matakan kandagarki, da na jan hankulan al'umma, kana lamarin bai kawo illa ga yanayin karko na zamantakewar al'umma ba.
Haka kuma, gamayyar kungiyar bunkasa kudancin kasashen Afirka ta SADC ta kira wani taron musamman na ministocin kiwon lafiyar mambobin kasashen gamayyar, don tattaunawa kan yadda za a iya fuskantar lamarin, idan cutar Ebola ta yadu zuwa kudancin kasashen na Afirka. (Maryam)