in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'in OMS ya jinjinawa taimakon Sin domin yaki da cutar Ebola a Afrika
2014-08-14 13:51:05 cri
Taimakon kasar Sin ya bayar da wani sabon yunkuri wajen yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika, in ji wani jami'in kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS a ranar Laraba. Kasar Sin ta bi sahun gamayyar kasa da kasa domin kara karfin yaki da Ebola a yammacin Afrika. Tallafin kasar ta fuskar kayayyakin likitanci, jami'an lafiya da kayayyaki sun zo a daidai lokacin da ake bukata, in ji Custodia Mandlhate, wakilin kungiyar OMS a kasar Kenya.

Tawagogin likitanci uku na kasar Sin da kowa ce take kunshe da kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa, da kwararru biyu a fannin cututtuka da kiyaye mutane daga kamuwa da cututtuka, kuma sun isa tare a ranakun Litinin da Talata a kasashen Guinee, Liberiya da Sierra Leone domin taimakawa yaki da cutar Ebola.

"Kasar Sin ita ma a shekarun baya ta ci nasarar fama da cutar murar tsuntsaye da SRAS. Wuraren dake cutar Ebola ta fi kamari na iyar amfani da kwarewar Sin wajen kawar da wannan annobar", in ji mista Mandlhate.

Baya ga wadannan kwararrun kiwon lafiya, Sin ta kuma aike da ton 80 na kayyayakin likitanci da magunguna a kasashen Guinee, Liberiya da Saliyo.

Haka kuma, mista Mandlhate ya nuna yabo kan tawagogin lafiya na kasar Sin dake aiki a kasashen Afrika domin taimakawa wajen yaki da cututttuka masu kashewa, tare da kara da cewa zuba jarin da kasar Sin ta yi kan ayyukan gine ginen kiwon lafiya a Afrika abin yabo ne. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China