Duk da furucin da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi, na amincewa a yi amfani da magungunan gwajin magance cutar Ebola a yammacin Afrika, a hannu guda wani shahararren masani na kasar Amurka ya yi gargadin cewa, amfani da irin wadannan magunguna zai iya kawo illa ga yammacin Afrika, ta fuskar tsananta dangantakar dake tsakanin wadanda suka kamu da cutar da kuma ma'aikatan jiyya.
A daya bangaren kuma shugaban cibiyar nazarin cututtuka masu gadari na Amurka Anthony Fauci, ya ce babu wani magani mai cikakken amfani da zai iya magance cutar da ake fusanta yanzu haka. A cewarsa matakin da ya fi dacewa a halin yanzu shi ne, gudanar da kandagarkin yaduwar cutar, tare da samarwa kasashen da ke fama da cutar tallafi.
A ganinsa, akwai 'yar yiwuwar samun bullar wannan cuta ta Ebola a sauran wurare, saboda yawancin kasashe ban da kasashen Afrika na da karfi sosai wajen ware wadanda suka kamu da cutar da yi musu jiyya.
Kaza lika za a iya dakile yaduwar cutar, duba da cewa ba ta yaduwa ta iska, sai dai ta hanyar nau'oin ruwan jikin mutum. (Amina)