in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta karbi magungunan gwaji kan cutar Ebola
2014-08-16 15:45:53 cri
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi magungunan gwaji kan yaki cutar Ebola daga wani masanin kimiyyya dan Najeriya da ba'a fayyace sunansa ba, in ji ministan kiwon lafiya Onyebuchi Chuku.

Mista Chuku ya bayyana cewa sauran abubuwan da za'a hada da wannan magani mai sunan Nanosilver za'a gabatar da su a nan gaba ga manema labarai. Babu wani nau'in cutar Ebola da aka gano daga wajen birnin Lagos, in ji ministan tare da jaddada cewa dukkan mutanen da ake zaton suna dauke da wannan cuta a sauran yankunan kasar ba su da wannan cuta. Haka kuma ya kara bayyana cewa jihar Cross River ba'a samu barkewar wannan cuta ba, inda ya kara da cewa ma'aikaciyar lafiya da aka tsare a asibiti a birnin Lagos da kuma ta yi tafiya zuwa jihar Enugu dake kudu maso gabashin kasar ta koma Lagos tare da mambobin iyalinta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China