Ita dai wannan mata ta bada jinya ne ga Patrick Sawyer dan asalin kasar Liberiyan nan da ya fara zuwa da cutar a jihar Ikko, ya kuma mutu a ranar 25 ga watan jiya, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka sanar.
Matar ta rasu ne da safiyar Alhamis din nan a babban asibitin gwamnati na Yaba dake Ikko, duk da cewa har yanzu ba'a fitar da wata sanarwa a hukumance ba tukuna.
Kafin haka wata mai aikin jinya da ita ma ta kula da lafiyar Sawyer kafin mutuwarsa ta rasu a makon da ya gabata, sannan wani ma'aikaci a ofishin kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS dake Ikkon shi ma ya rasu ranar Talatan nan da ta shige.
Gwamnatin Nigeriya dai a ranar Litinin ta riga tabbatar da cewa yanzu haka akwai rahoton mutane 10 da suka kamu da cutar ban da wadansu 177 da ake sa musu ido a gani ko akwai alamu a tare da su.
Jumma'an da ta gabata, shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da dokar ta baci a kan cutar, inda ya ce za'a fitar da kudi Naira biliyan 1.9 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 11.6 domin gudanar da ayyukan ba da kariya da hana yaduwar cutar. (Fatimah)