in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta dakatar da shigowar jiragen ruwan dake fitowa daga kasashen dake fama da Ebola
2014-08-15 10:31:04 cri
Tashar ruwan birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire ta dakatar da shigowar jiragen ruwan dake fitowa daga kasashen dake fama da cutar Ebola, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wata majiya mai tushe daga hukumomin tashar ruwan. Labarin na nuna cewa, hukumomin tashar ruwan sun jaddada cewa duk wani marasa lafiya dake nuna alamu irin na cutar Ebola a cikin jirgin ruwa, ya zama dole a sanar da hukumomin tashar ruwan Abidjan da za su iyar tantance fa'idar barin jirgin ruwa shigowa, duk ma daga inda ya fito. Babu wani nau'in cutar Ebola da aka gano a kasar Cote d'Ivoire, amma duk da haka kasar na cikin shirin ko ta kwana. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China