Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta ce barkewar cutar Ebola da yaduwar da take yi a wurare da dama tsahon lokaci, na sanya jama'a damuwa matuka, sai dai duk da hakan akwai bukatar kaucewa amfani da jita-jitar da ke yaduwa kan yiwuwar samun rigakafin cutar ta Ebola.
WHO ta ce, ganin yadda mafi yawan wadanda suka kamu da cutar ke mutuwa, hadi da rashin takamaiman maganin cutar ya sanya jama'a tsorata da ita. Hakan ya kai ga yada jita-jitar samun magani dake iya warkar da cutar.
Sai dai a cewar wannan hukuma duk wani magani da za a yi amfani da shi game da cutar, kamata ya yi a ce an riga an gwada shi, bai kuma kamata a yi amfani da maganin da hukumomin sa ido ba su amince da shi ba. Game da magungunan gwaji da ake fatan amfani da su ga bil'adama, hukumar ta ce hasashe ne kawai ake yi kan amfanin su, babu wasu shaidu dake tabbatar da cikakken amfani, ko ingancinsa, balle illar da zai iya haifarwa.
Dadin dadawa, WHO ta ce, kwararrun ta sun amince bisa halin da ake ciki, a yi amfani da wasu magunguna na gwaje, duk da babu isassun irin wadannan magunguna. Kana mawuyaci ne nan da badi a iya samar da sahihin magani ko rigakafin wannan cuta ta Ebola. (Amina)