in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da tallafi domin yaki da cutar Ebola
2014-08-16 16:47:18 cri

Ranar 15 ga wata, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Saliyo Abu Bakar Fofanah ya gana da tawagar masanan kasar Sin masu ilmin kiwon lafiyar al'umma, inda ya ce, yanzu ayyukan yaki da cutar nan ta Ebola ba su tafiya daidai da yadda cutar ke yaduwa a kasarsa. Ana matukar bukatar kasashen duniya da su kara ba da tallafi.

Abu Bakar Fofanah ya kuma yi wa kasar Sin godiya game da kayayyakin taimako da gwamantin Sin da jama'ar kasar suka bayar cikin lokaci tare da turawa wata tawagar masana. Ya kara da cewa, za a rarraba kayayyakin taimakon da gwamnatin Sin ta bayar a cikin asibitoci karkashin shugabancin gwamnatin Saliyo, inda likitoci da masu ba da jinya za su yi amfani da su wajen yaki da cutar.

Har wa yau, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta ba da wata sanarwa a ranar 15 ga wata cewa, an ce, wai wasu kayayyaki ko aikace-aikacen da aka yi na iya kare mutane daga kamuwa da cutar Ebola ko kuma suna iya warkar da masu kamuwa da cutar. Hakan ba daidai ba ne, jita-jita ne ke nan. Watakila kafin shekarar 2015 mai zuwa ne ba za a iya samun allurar yin rigakafin cutar Ebola ba, wadda za a gwada ita daga dukkan fannoni sa'an nan za a amince da ita.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China