Shugabar sashen yin kashedi da tinkarar halin dokar ta baci ta WHO Isabelle Nuttal ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, cutar Ebola ta sha bamban da cutar mura da tarin fuka, ba ta yaduwa ta iska, sai dai ana kamuwa ta hanyar yin mu'amala kai tsaye kawai. Kana cutar tana iyar yaduwa bayan da alamun kamuwa da cutar suka bullo. Don haka, idan wani mutum dake da alamun kamuwa da cutar yana cikin jirgin sama a sararin samaniya, hadarin kalilan ne na yiwuwar sauran fasinjoji da ma'aikatan jirgin su taba ruwan jikin wannan mutum kai tsaye.
Bisa sabuwar kididdigar da hukumar WHO ta yi, an ce, ya zuwa ranar 11 ga wata, mutane 1975 na kasashen Guinea, Liberia, Saliyo da Nijeriya sun tabbatar da kamuwa da cutar, ko aka zarge su da kamuwa da cutar, kuma 1069 daga cikinsu sun rasa rayukansu. (Zainab)