Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin sa Stephane Dujarric, ya kara da cewa WHO na bukatar goyon bayan dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, a kokarin ta na dakatar da yaduwar wannan cuta mai saurin kisa.
A shekarar da ta gabata dai wannan cuta ta Ebola ta yi barna mafi yawa ne kasar Guinea, kafin daga bisani ta yadu zuwa wasu karin kasashen dake yammacin Afirka.
A bana kuwa, kididdigar baya bayan nan da hukumar WHO ta fitar ta nuna cewa, daga 10 zuwa 11 ga watan nan na Agusta, an samu karin mutane 128 da suka kamu da wannan cuta, baya ga wasu mutane 56 da cutar ta hallaka.
Bisa jimilla dai mutane 1,975 ne aka tabbatar sun karbu da wannan cuta a bana, wadanda suka fito daga kasashen Guinea, da Liberia, da Najeriya da kuma Saliyo, cikin su kuwa tuni mutum 1,069 suka riga mu gidan gaskiya. (Saminu)