in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka ta sha satar labaran kamfanonin kasashe da dama, in ji wata jaridar Amurka
2014-05-22 14:38:25 cri

A ranar Laraba 21 ga wata, Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, tun a baya kasar Amurka ta sha satar labaran wasu kamfanoni na kasa da kasa. Inda ta kan yi hakan domin kara samar da fifiko tattalin arziki kan ragowar kasashe.

Tuni dai wasu jami'an kasar suka amince da cewa, hukumar tsaron kasar ta NSA ta kan sanya ido kan wakilai dake shawarwari kan cinikayya na kasashen Turai da Asiya bisa son ranta, domin taimakawa jami'an kasarta a wannan fanni.

Labarin ya ce, domin samun labaran da take bukata kan sojojin kasar Sin, hukumar NSA ta taba shiga tsarin kwamfutocin kamfanin wayoyin sadarwa na China Telecom. Haka zakila, hukumar ta sha jin leken wasu manyan kamfanoni, ciki har da kamfanin Huawei, da kamfanin Pacnet, mai kula da ayyukan da ke da nasaba da manyan wayoyin sadarwa da ake shimfidawa karkashin teku.

Bugu da kari, wakilin kwamitin kungiyar EU mai kula da ayyukan yaki da babakere Joaquin Almunia, shi ma yana kan idonta.

Bisa labarin da jaridar ta bayar kuma, an ce, hukumar NSA na sha'awar kamfanonin man fetur dake karkashin jagorancin gwamnatocin kasashe daban daban, ciki har da na kasashen Brazil, Saudi Arabia, Afirka, Iran da kuma Mexico.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China