in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi kashedi ga kasashen yankin gabas ta tsakiya da su daina tsoma baki kan halin da Iraki take ciki
2014-06-26 14:38:44 cri
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya yi kashedi ga kasashen dake yankin gabas ta tsakiya da su daina tsoma baki kan halin da Iraki take ciki ta hanyar tura soja, don magance tsanancewar rikicin addini tsakanin al'ummar kasar.

Kerry ya bayyana hakan a gun taron ministocin harkokin waje na kasashe membobin kungiyar tsaron NATO a birnin Brussels a ranar 25 ga wata. Kerry ya kuma bayyana cewa, ana bukatar hukumomin Bagadaza su dauki matakan tabbatar da karfin sojojin gwamnatin kasar, ta yadda za su cimma nasarar fatattakar masu tsattsauran ra'ayi, da dakile hanyar taimakon da suke samu daga kasashen waje. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China