A yayin taron manema labaru da suka shirya tare bayan shawarwarin, shugaba Obama ya ce, har kullum gwamnatin Amurka na ganin, tsibirin Diaoyu na hannun gwamnatin Japan a halin yanzu, wanda Amurka za ta tabbatar da tsaronsa. Amma Obama ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka ba ta da wani matsayi kan mulkin kan tsibirin na Diaoyu.
Har wa yau, shugaba Obama ya ce, kasashen Amurka da Sin sun kulla dankon dangantaka a tsakaninsu, kana sun samu moriyar bai daya a fannoni daban daban. Amurka za ta ci gaba da mara wa Sin baya wajen samun ci gaba cikin lumana. Ya kuma gaya wa firaministan na Japan fatansa cewa, kada a rura wuta a batutuwa masu ruwa da tsaki, kuma ya goyi bayan kulla aminci a tsakanin Sin da Japan, a kokarin warware batutuwan ta hanyar tattaunawa.(Tasallah)