Yayin wani taron 'yan jaridu da ofishin AU da WHO suka gudanar, kwamishinoninsu sun bayyana cewa mahukuntan bangarorin biyu, na da fargabar yaduwar cutar zuwa wasu karin kasashen dake yammacin Afirka, muddin ba a gaggauta daukar matakan da suka wajaba ba.
Don haka a cewar jami'in AU ta gabatar da shawarar fidda managartan tsare-tsare, da za su baiwa daukacin kasashen dake wannan yanki ikon tinkarar wannan babban kalubale.
Tun dai cikin watan Afirilun da ya shude ne taron hadin gwiwar ministocin kungiyar AU da na hukumar WHO, ya fidda wata sanarwa a birnin Luandan kasar Angola, wadda ta nuna bukatar dake akwai ga kasashen Afirka, na daukar matakan kandagarkin yaduwar cutar ta Ebola.
Yanzu haka dai wannan cuta ta riga ta yadu a kasashen Guinea, da Liberia, da Saliyo, da kuma tarayyar Nigeria. (Saminu)