in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Ukraine sun fara tuntubar yankunan da ke gabashin kasar
2014-06-23 14:23:07 cri

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sanar da shirin wanzar da zaman lafiya a ranar 20 ga wata, inda ya shelanta kudurin tsagaita bude wuta a yankunan da ke gabashin kasar har tsawon mako guda.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar suka bayar, an ce, a ranar 21 da ta 22 ga wata, a gabashin kasar Ukraine, sojojin gwamnatin, da na dakarun yankin, ba su bi umurnin shugaba Poroshenko na tsagaita bude wutar ba. Kazalika shafin yanar gizo na shugaban kasar Ukraine ya fidda wata sanarwa a daren 21 ga wata, wadda ta bayyana cewa, kasarsa na shirin daukar dukkan matakai don neman maido da cikakkun yankunan kasa, inda za a bi matakan lumana a matakin farko.

A wani bangare kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zanta ta waya da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel a jiya Lahadi, inda ya jaddada cewa, idan ana son cimma wannan buri na shugaban kasar Ukraine, to da farko ya kamata a tsagaita bude wuta, sa'an nan ya wajaba mahukuntan kasar sun yi shawarwari da yankuna masu adawa ba tare da bata lokaci ba. Haka zakila, gwamnatocin Faransa da Jamus sun bayar da sanarwa a wannan rana, inda suka yi kira ga bangarori daban daban na Ukraine da suke tada hargitsi da su kauracewa nuna karfin tuwo. Kasashen sun kuma bukaci shugaba Putin da ya taimaka wa hukumar kasar Ukraine wajen yin shawarwari tare da dakarun dake gabashin kasar.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China