A wannan rana kuma, majalisar dattijan kasar Rasha ta kada kuri'u, tare da zartas da kudurin soke bada izinin gudanar da ayyukan soja a kasar Ukraine, kamar wanda shugaban kasar Rasha Vładimir Putin ya bada shawara.
A wani ci gaba kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasar Sin ta yaba da shawarar shugaba Putin, da kuma kokarin da bangarori daban daban ke yi, wajen warware rikicin kasar Ukraine, tana mai imani da cewa wadannan matakai za su taimakawa wajen warware rikicin ta hanyar siyasa.
A daya bangaren kuma shugaban kasar Faransa François Hollande, da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, sun tattauna ta wayar tarho tare da shugaban kasar Rasha, da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko, inda Hollande da Merkel suka yi kira ga shugabannin Rasha da na Ukraine, da su hada kansu, da aiwatar da tsagaita bude wuta.
Bugu da kari ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar tsaron NATO, sun yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Ukraine, inda suka cimma daidaito ga batun baiwa kungiyar tsaro ta NATO damar daukar matakai na taimakawa kasar Ukraine, wajen kara kiyaye tsaro. (Zainab)