in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba ta yarda da daukar matakin soja ta hanyar da ba ta dace ba
2014-07-31 20:32:36 cri

Ranar 30 ga wata, kasar Isra'ila ta harba bama-bamai kan wani sansanin 'yan gudun hijira da MDD ta kafa a cikin wata makarantar da ke arewacin zirin Gaza, inda mutane da dama suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata. A cewar Ban Ki-moon, babban sakataren MDD, harba bama-baman da Isra'ila ta yi bai dace ba, ya zama tilas Isra'ila ta dauki alhakin lamarin.

Dangane da lamarin, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis 31 ga wata cewa, harba bama-baman da Isra'ila ta yi kan makarantar da ke karkashin kulawar MDD ta girgiza kasar Sin sosai, kuma Sin ta yi tir da abin da Isra'ila ta yi. Kasar Sin ta yi kira ga bangarori 2 masu gwagwarmaya da juna da su amsa kiran kasa da kasa, su tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba. Ko kusa kasar Sin ba ta yarda da daukar matakin soja ta hanyar da ba ta dace ba, haka kuma ba ta yarda da kai hari kan gine-gine da ke karkashin shugabancin MDD ba, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China