in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta kama wasu mutanen da ake zarge su da aikata laifin kashe matashin Palesdinu
2014-07-07 10:08:07 cri
A ranar 6 ga wata, 'yan sandan Isra'ila da hukumar kiyaye tsaron kasar wato Shin Bet sun kama wasu Yahudawan da aka zarge su da a hannu a yi garkuwa da kashe wani matashin Palesdinu mai suna Mohammed Abu Khedir.

Hukumar ta Shin Bet ta bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ta ce, ana bincike kan wadannan Yahudawa, sai dai babu wasu shaidu da aka gabatar a zahiri a halin yanzu da za su tabbatar da hakan.

Shugaban kasar Palesdinu Mahmoud Abbas ya yi kira ga MDD da ta kafa kwamitin yin bincike na musamman don yin bincike kan ayyukan ba-dadi da Isra'ila ta yiwa jama'ar Palesdinu. Kana ya bayyana cewa, daya daga cikin ayyukan kwamitin shi ne yin bincike kan lamarin kisan matashin Palesdinu. Haka kuma, shugabannin Palesdinawa sun shirya sosai don yaki da ayyukan da sojojin Isra'ila suka yi a zirin Gaza da gabar yamma ta kogin Jordan.

Lamarin kisan Khedir ya haifar da mummunan rikici tsakanin al'ummar Palesdinawan dake gabashin Kudus da 'yan sandan Isra'ila. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China