Ban Ki-moon ya bayyana wa 'yan jarida a cibiyar MDD dake birnin New York cewa, koda yaka shi da sauran shugabannin kasa da kasa da na yankin sun yi kira ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza, amma halin da yankin ke ciki yana ci gaba da tsananta, abin da Mr Ban ya nuna takaicinsa a game da hakan.
A cikin awoyi 24 da suka gabata, an samu labarin mutuwar wasu fararen hula, ciki har da yara hudu a sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai ga wani rairayin bakin teku dake zirin Gaza. Dangane da hakan Mr Ban ya jaddada cewa, hanyar aikin soja ba za ta warware rikicin dake tsakanin Palesdinu da Isra'ila ba, ya kalubalanci Isra'ila da ta kara yin kokarin magance mutuwa da raunatar fararen hula.
Bangaren sojojin tsaron kasar Isra'ila ya sanar a ranar Alhamis 17 ga wata cewa, a wannan daren, sojojin sun tura sojojin kasa, masu amfani da motocin sulke, injiniya, masu sarrafa igwa da kuma sojojin musamman zuwa zirin Gaza da kai hari ga zirin a karkashin kariyar sojojin ruwa da sama suka yi musu. (Zainab)