Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Isra'ila suka bayar a wannan rana, Isra'ila ta fitar da shirinta na gina dakunan kwana 1200, domin kasancewa matsugunnan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan, da kuma gabashin birnin Kudus. Haka kuma a wannan makon da muke ciki, gwamnatin Isra'ila za ta kara amincewa da gina dakunan kwana 800 a wannan yanki.
Kamfanin dillancin labarai na al'ummar Palesdinu Maan, ya ruwaito Mr. Erekat, na cewa Isra'ila ta yi haka ne domin gurgunta shirin shawarwari zagaye na biyu da za a yi ranar 14 ga wata tsakanin bangarorin biyu, tare da burin ganin Palesdinu ta bar teburin shawarwarin.
Don da hakan dai Mr. Erekat, yana sa ran ganin wannan shiri na shawarwari ya haifar da zaman lafiya, kuma ya ce, Palesdinu na son ci gaba da kokarin tattaunawa a cikin watanni shida zuwa tara masu zuwa, sai dai yace yanzu lokaci ya yi da gwamnatin Isra'ila ta zabi hanyar yin shawarwari da nuna aniyarta don cimma wannan buri.(Kande Gao)